Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iidr an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro domin yin nazari dangane da kissoshin da ke cikin surat Yusuf da kuma irin darussan da ke cikin wannan sura a rayuwar mutane ta zamantakewa. Bayanin ya ci gaba da cewa bangaren gudanar da bincike kan tarihi da addininai na jami'ar birnin London shi ne ya dauki nauyin shiya gudanar da zaman taron. 606113