Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da jaridar alraya ta kasar Qatar ta buga a shafinta na yanar gizo ta bayyana cew, za a fara gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki a matsayi na kasa da kasa a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, da ke samun halartar makarnta da mahardata. Taron gasar zai samu halartar wasu daga cikin wakilan cibiyoyin addini na kasashen turai musamman ma daga kasar Birtaniya. Minista mai kua da ayyukan addini na kasar Qatar shi ne zai jagoranci bude zaman taron gasar. 606790