IQNA

Taro Kan Hakkokin Imam Zaman A Mahangar Kur'ani

15:09 - July 01, 2010
Lambar Labari: 1949273
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani zaman taro da zai bahasi kan hakkokin Imam Zaman a mahangar kur'ani mai tsarki a Saudiyya.
Kamfanin dilancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga tashar yada labarai ta Rasid an bayyana cewa, za a fara gudanar da wani zaman taro da zai bahasi kan hakkokin Imam Zaman a mahangar kur'ani mai tsarki, wanda wata cibiyar mabiya mazhabar iyalan gidan manzo ta shirya a Saudiyya. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai mayar da hanakali ne wajen karfafa bincike kan Imam hujja, domin sanin hakkokinsa a kan al'umma, musamman a mahangar kur'ani mai tsarki. 606847




captcha