IQNA

An Shiga Bangaren Karshe A Gasar Kur'ani A Kasar Yeman

15:06 - July 01, 2010
Lambar Labari: 1949274
Bangaren kasa da kasa; An shiga bangaren karshe na gasar karatun kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Yeman, wadda ma'aikatar harkokin kur'ani ta kasar ta shirya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Yeman saba a shafinsa na yanar gizo cewa, an shiga bangaren karshe na gasar karatun kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Yeman, wadda ma'aikatar kula da harkokin kur'ani ta kasar ta shirya gudanarwa. Bayanin ya kara da cewa fadar shugaban kasar ta taka gagarumar rawa wajen taimaka ma ma'aikatar kula da harkokin addini wajen shirya gasar. Yanzu haka dai makaranta da mahardata ne suka shiga bangaren karshe na gasar.606810



captcha