Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran bernama an bayyana cewa, gwamnan lardin Sabah a kasar Malazia ya fadi cewa za a bude wata jami'a ta hardar kur'ani mai tsarki a lardin, da za ta mayar da hanakali wajen samar da mahardata kur'ani. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan jami'a za ta kunshi bangarori daban-daban na harda da kuma karatu.606874