Kamfanin dillancin lambaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar kasar hadaddiyar daular larabawa ta Ittihad cewa, za a gudanar da taron wakilan kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Jidda na kasar Saudiyya a cikin wannan mako. Taron zai yi dubi ne kan muhimman batutuwa da suka danganci lamurran cikin gida na kasashen musulmi da kuma larabawa, musamman ma batun sulhu tsakanin larabawa da haramtacciyar kasar yahudawa. 606884