Bangaren al'adu da fasaha; Musulmin kasar Azarbaijan sun nuna rashin amincewarsu da buga littafin ayoyin shaidan a cikin wata takarda da ke dauke da labarai da ake bugawa duk wata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na birlik an bayyana cewa, musulmin kasar Azarbaijan sun nuna rashin amincewarsu da buga littafin ayoyin shaidan a cikin wata takarda da ke dauke da labarai da ake bugawa duk wata. Bayanin ya ci gaba da cewa wata jam'iyar siyasa a kasar ta dauki matakin mika kokenta ga bababn kwamitin kula da harkokin addini na kasar domin nuna rashin amincewarsu da hakan. 607056