IQNA

Shugabanin Kasashen Musulmi 20 Za Su Gudanar Da Zama A Syria

Bangaren fikira da ilimi; A yau ne kasashen musulmi 20 za su fara gudanar da wani zamansu a birnin Damascus na kasar Syria domin tattauna wasu batutuwa da suka danganci kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran tashrin ya habarta shafinsa na yanar gizo cewa, a yau ne kasashen musulmi 20 za su fara gudanar da wani zamansu a birnin Damascus na kasar Syria domin tattauna wasu batutuwa da suka danganci kasashen musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban kasar Syria Bashar Asad shi ne zai jagoranci zaman bude taron a yau. Muhimman abubuwan da taron zai mayar da hanakali kansu akwai batun rikicin palastinawa da haramtacciyar kasar Isra'ila, da kuam wasu daga cikin mattsalolin kasashen musulmi. 606856