IQNA

An Kammala Gasar Hardar Kur'ani A Kasar Mauritania

15:25 - July 03, 2010
Lambar Labari: 1950101
Bangaren kasa da kasa; An kammala wata gasar hardar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Nuwak shaut na kasar Mauritania wadda aka gudanar a matsayi na kasa baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran gwamnatin Mauritaniya an habarta cewa, an kammala wata gasar hardar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Nuwak shaut na kasar Mauritania wadda aka gudanar a matsayi na kasa baki daya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa ta samu halartar wasu daga cikin fitattun mahardatan kur'ani na kasar, wadanda suka samu lambar yabo bayan kammala gasar. 607750



captcha