IQNA

Bahasi Kan Tarihin fitattun Makaranta Kur'ani Na Duniya A Qatar

15:25 - July 03, 2010
Lambar Labari: 1950104
Bangaren kasa da kasa; A cikin watan Ramadan mai zuwa ne za a gudanar da wani shiri a gidan radiyon kasar Qatar kan binciken tarihin fitattun makaranta kur'ani na duniyar musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar alraya ta kasar Qatar ta rubuta a shafinta cewa, a cikin watan Ramadan mai zuwa ne za a gudanar da wani shiri a gidan radiyon kasar Qatar kan binciken tarihin fitattun makaranta kur'ani na duniyar musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri zai mayar da hankali ne kan irin rawar da makarantan suka taka wajen yada ilmin karatun kur'ani a duniyar musulmi, da kuma irin yadda suka sha gwagwarmayar neman ilmin kafin su kai ga matsayin da suka samu kansu. 607773



captcha