IQNA

Cibiyar Kasa da Kasa Ta Hidima Ga Sunnar Ma'aiki(SWA)

16:50 - July 03, 2010
Lambar Labari: 1950170
Bangaren kasa da kasa; a ranar goma ga watan Tir na wannan shekara ce hadin guiwar cibiyoyin bincike na musuluncu Al-azhar suka amince da kafa wata uwar cibiya ta Aazhar lisunna wa siratul Nabawi (SWA) da za ta rika yin hidima kan sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa tsarkaka.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Iran ikna bayan ta nakalto daga jaridar Saudiya ta Alwatan ta watsa rahoton cewa; a ranar goma ga watan Tir na wannan shekara ce hadin guiwar cibiyoyin bincike na musuluncu Al-azhar suka amince da kafa wata uwar cibiya ta Aazhar lisunna wa siratul Nabawi (SWA) da za ta rika yin hidima kan sunnar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa tsarkaka.Ita dai cibiyar Azhar walsiratul Nabawiyua (SWA) yau shekaru goma sha bakwai da suka gabata ken an da kafata da burin bada amsa da maida martani kan gurbata sirar ma'aiki amma ya zuwa yanzu kwalliya bat a biya kudin sabulu ba.


607797
captcha