Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta da ke kasar Labanon ta watsa rahoton cewa; shugaban jam'iyar Imam Sadik (AS) a kasar Labanon yayi nuni da kokarin mai yawa kuma mai muhimmanci da malaman jablul Amil a kasar Labanon sun taka wajen yin hidima ga addinin Musulunci da kuma muhimmiyar rawar da suka taka wajen raya maktabar fikihu ta imam Ja'afar Sadik (AS). A ranar goma ga watan Tir na wannan shekara ce ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya asheikh Hasan Bagadadi a lokacin wani taron juyayi na Sheikh Musa Ja'afar Mugniya yayi wannan bayani.
607830