Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bayan kammala kiran salla na'ibin limamamin juma'a a birnin Tehran da ya jagorancin sallar Ayatollah Imam Kashani ya fara gabatar da hudubarsa a gaban dubban daruruwan masallata. A cikin hudubar ya farad a kawo muhimman mas'aloli na shari'a da suka danganci rayuwar mutane ta zamantakewa.
A wani banagare kuma ya tabo batutuwa da suka danganci irin shishigi da yahudawan sahyuniya suke kan abubuwa masu tsarkia cikin addinin Musulunci a yankunan da suka mamaye na musulmi. Haka nan kuma ya tabo batun shahadar Ayatollah Beheshti tare da sauran mutane 72 da suka shahada tare da shi sakamakon kai harin da munafukai suka yi kansu.
Malamin ya yi kan batun takunkumin da Amurka da masu yi mata amshin shata suka kakaba kan Iran, tare da bayyana shi da cewa ba shi da wani amfani ko tasiri a kan kasarsa, tafuskokin tattalin arziki hatta ma ta fuskacin siyasa, ya ce irin wannan ne ma zai kara musu kaimi wajen gaba da fadada bincike na ilimi domin ci gaban al'ummarsu.
607726