Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na albashir ya habarta cewa, ana shirin fara gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a garuruwan kasar Birtaniya, wadda msulmin kasar za su gudanar karkashin shirin cibiyoyin kur'ani na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin wadanda za su shiga cikin gasar musulmi mazauna kasar, shekarunsu suka fara daga goma zuwa shekaru talatin, inda aka rarraba bangarorin da za a gudanar da gasar harda a kansu bisa sgekaru, inda 'yan shekaru 10 zuwa 16 za su daga juzui na daya, sauran kuma daidai da shekarunsu har zuwa ga wadanda za su yi hardar kur'ani baki daya.
608111