IQNA

Taro Kan Harkokin Tattalin Arzikin Musulunci A Faransa

17:22 - July 04, 2010
Lambar Labari: 1950943
Bangaren kasa da kasa; A cikin watan gobe za a gudanar da wani zaman taro a birnin paris na kasar Faransa kan makomar tattalin arzikin musulunci a kasar da kuma shawarwarin masana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na sapphire news ya bada labarin cewa, a cikin watan gobe za a gudanar da wani zaman taro a birnin paris na kasar Faransa kan makomar tattalin arzikin musulunci a kasar da kuma shawarwarin masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi.

Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin shugabannin cibiyoyin musulmi na kasar faransa da suka hada da fitattun malaman jami'a su ne suka shirya gudanar da zaman taron.

Wadanda suke son samun cikakkiyar masaniya kan taron suka iya tuntuba da wannan addreshi na email: contact@orbital-information.

608134
captcha