IQNA

Taron Mabiya Mazhabar Shi'a A Jahar Florida Ta Kasar Amurka

17:21 - July 04, 2010
Lambar Labari: 1950946
Bangaren kasa da kasa; Mabiya mazhabar iyalan gidan manzo mazauna jahar Florida a kasar Amurka za su fara gudanar da wani zaman taronsu a birnin Miamy a cikin wannan mako.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo palmbeachpost an bayyana cewa, mabiya mazhabar iyalan gidan manzo mazauna jahar Florida a kasar Amurka za su fara gudanar da wani zaman taronsu a birnin Miamy a cikin wannan mako.

Rahoton ya kara da cewa, za a gudanar da zaman taron bisa wani shri na babbar hadakar cibiyoyin mabiya mazhabar shi'a da ke jahar, da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci harkokinsu na addini a cikin kasar.

Bayannan kuma za a gudanar da jawabai daga malamai daban-daban mazauna jahar, daga cikinsu kuwa hard a mambobin kwamitin babban masallacin jahar Florida, haka nan kuma mambobin cibiyar musulmi ta jahar Olondo su ma za su halarci zaman taron.

608150





captcha