Bangaren kasa da kasa; Za a gina wani babban masallaci A kasar Algeria da zai dauki masallata akalla dubu dari da ashiri 120,000 wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar ta dauki nauyin ginawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar alwatan da ake bugawa akasar Kuwait ta bada labarin da ke cewa, za a gina wani babban masallaci da zai dauki masallata akalla dubu dari da ashiri 120,000 wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar ta dauki nauyin ginawa, wanda shi ne masallaci mafi girma a duk fadin kasar.
Minista mai kula da harkokin addinin musulunci a kasar ta Algeria ya bayyana cewa, yanzu haka an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata, domin fara wannan babban aiki da zai dauki tsawon lokaci a nan gaba kafin kammala shi.
608258