Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran kur'ani na muzn ya bada rahoton cewa, an fara gudanar da wani shiri na horar da mata mabiya mazhabar shi'a karatun kur'ani mai tsarki a garin Hufuf na lardin Ihsa da ke gabacin kasar Saudiyya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri yana samun halartar mata daga sassa daban-daban na yankin.
Babbar manufar gudanar da shirin bayar da horon dai ita ce kara bayar da dama ga mata su samu hanyoyi na kara karfafa kansu wajen karatun kur'ani da kuma sanin ma'noninsa.
608335