IQNA

Za A Nuna Wani Shirin Talabijin Kan Qods A Syria

Bangaren fasaha da al'adu; Masu kula da tsara fina—finan talabijin a kasar Syria za su nuna wani shirin fim kan masallacin Qods mai alfarma a cikin watan Ramadan na wannan shekara.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar ittihad ta kasar hadaddiyar daular larabawa ta rubuta a cikin bugunta na wannan makon cewa, masu kula da tsara fina—finan talabijin a kasar Syria za su nuna wani shirin fim kan masallacin Qods mai alfarma a cikin watan Ramadan na wannan shekara, kamar dai yadda suka saba fitar da silsilar fina-finai a kowace shekara.

Bayanin ya ci gaba da cewa a wannan karon shirin silsilar fim din shekara na watan Ramadan zai sha banbam da sauran wadanda aka gudanar a shekarun baya, bisa la'akari da halin da ake ciki yanzu a yankin palastinu baki daya.

Daga cikin muhimman abubuwan da silsilar fim ta bana za ta mayar da hankali kansu har da tsananta kame-kamen da haramtacciyar kasar Isra'ila ke kan palastina a cikin lokutan nan, da kuma rushe wasu bangarori na masallacin Qods, gami da mayar da wasu wurare masu tsarki na musulunci a cikin kayan tarihin yahudawa.

608422