Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kur'ani na Muzni daga shafinsa na yanar gizo an bayyana cewa, za a gudanar da wani shirin bayar da horon karatun kur'ani mai tsarki a birnin Karbala mai alfarma da ke kudancin kasar Iraki, wanda zai kebanci matasa 'yan makaranta.
Bayanin ya kara da cewa, wannan shirin bayar da horo cibiyar kula da shirya gasar hardar kur'ani ta kasa ita ce ta shirya gudanar da shi har tsawon watanni hudu a nan gaba. Yanzu haka daruruwan yara 'yan makaranta ne suka yi rijistar sunayensu domin samun wannan horo da zai taimaka musu wajen koyon sahihin karatun kur'ani. 608865