Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Bernama a shafinsa na yanar gizo an bayyana cewa, ministan harkokin addinin Musulunci a kasar Malazia ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta sha alwashin ganin ta bunkasa harkokin karatu da hardar kur'ani mai tsarki a fadin kasar ta Malazia.
Ahmadsha Abdullah gwamnan lardin sabah ya bayyana cewa, yanzu haka gwamnatinsa na shirin daukar bakuncin wata gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da za a gudanar a kasar na da wasu 'yan watanni masu zuwa.
609076