Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na nasij an bayyana cewa, an kaddamar da wani shirin nazari kan sirr manzon Allah (SAW) a jami'ar adabi da bincike kan halayen dan adam ta birnin Madina mai alfarma da ke kasar Saudiyya.
Bayanin ay ci gaba da cewa shiri zai mayar da hanakali kan gudanar da bincike da kuma bahasi kan sirar manzo da kuma abubuwan da suka wakana a lokacin rayuwarsa da yadda ya tafiyar da su, tare ad dogaro da dalilai masu karfi kan sahihancin ruwayya.
Ya kara da cewa yanzu haka masana daga sassa daban-daban na jami'on kasashen musulmi sun nuna cewa a shirya suke shiga cikin wannan nazari. Bayan kammala shirin za a buga dukkanin abubuwan da aka fitar a matsayin sakamakon nazarin.
608854