IQNA

Jam'iya Mai Mulki A Turkiya Ta Goyi Bayan Dauke Dokar Hana Saka Hijabi A Jami'a

17:23 - July 05, 2010
Lambar Labari: 1951723
Bangaren siyasa da zamantakewa; shugaban gungun jam'iyar adala da bunkasa ta kasar Turkiya kuma jam'iya mai mulki a wannan kasa ta bayyana amincewarta na goyan bayan shirin doka ta watsi da dokar hana sanya hijabi a jami'o'in kasar da jam'iyar yan kasa ke son gabatarwa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna daga reshenta da ke kasar Turkiya bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Al'alam ta watsa rahotonb cewa; shugaban gungun jam'iyar adala da bunkasa ta kasar Turkiya kuma jam'iya mai mulki a wannan kasa ta bayyana amincewarta na goyan bayan shirin doka ta watsi da dokar hana sanya hijabi a jami'o'in kasar da jam'iyar yan kasa ke son gabatarwa.Sa'ad Kalic shugaban gungun jam'iyar ta Adalci da ci gaba ta kasar Turkiya ya bada wannan labari.

608952
captcha