IQNA

Za A Bude Wani Kwalejin Koyon Karatun Kur'ani A Yemen

17:38 - July 05, 2010
Lambar Labari: 1951732
Bangaren kasa da kasa; Za a bude wani kwalejin koyon karatun kur'ani mai tsarki a kasar Yeman a yau a birnin Sa'a fadar mulkin kasar, taron da zai samu halartar malamai da jami'an gwamnatin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga daga shafin yanar gizo na kamfanin dillancin labaran saba an habarta cewa, za a bude wani kwalejin koyon karatun kur'ani mai tsarki a kasar Yeman a yau a birnin Sa'a fadar mulkin kasar, taron da zai samu halartar malamai da jami'an gwamnatin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan kwalji zai taka gagarumar rawa wajen samar da makaranta kur'ani a fadin kasar, ta yadda za su samu kyakyawan ilimin kur'ani daga asasi.

608818
captcha