IQNA

Yan Shi'a A Zimbabwe Za Su Raya Ranar Mab'ath Da Taro

15:30 - July 06, 2010
Lambar Labari: 1952328
Bangaren harkokin kur'ani" yan shi'a a kasar Zimbabwe ta hanyar gudanar da taro za su raya rana da daren da aka aiki ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.
Cibiyara da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga hukumar da ke kula da yada al'adun Iran a ketare ta watsa rahoton cewa; yan shi'a a kasar Zimbabwe ta hanyar gudanar da taro za su raya rana da daren da aka aiki ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka. Kuma wannan taro za a gudanar da shi ne a ranar sha takwas ga watan Tir na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya bayan sallar juma'a a masallacin Imam Khomeini ® a garin Kaduma.



609944
captcha