IQNA

Kan Rasuwar Ayatullahi Fadllullah

15:29 - July 06, 2010
Lambar Labari: 1952331
Allah ya yi wa babban Shehin Malamin nan Ayatullah Sayyed Muhammad Hussein Fadlallah rasuwa a yau lahadi a birnin Beirut bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Shehin Malamin dan kimanin shekaru 74 a duniya, a lokacin rayuwarsa ya kasance mai gwargwarmaya da kuma fada da ayyukan zalunci da HKI da kuma Amurka ke aikatawa a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma sauran kasashe na duniya. A game da irin yadda yake nuna adawa da bakar siyasar Amurka da kuma gwamnatin mamaya ta Isra'ila, wannan ya sa sau da dama hukumar leken asiri ta Amurka wato CIA ta yi yunkurin kashe shi cikinsu kuwa har da shirya wani harin bam da niyyar kashe shi a ranar 8 ga watan Maris na 1985 a birnin Beirut, harin da ya yi snadiyyar mutuwar akalla mutane 80.
Haka zalika marigayi Fadlallah ya kasance mutumin da ake matukar girmamawa a duniyar musulmi musamman ma mabiya mazhabar Shi'a, da kuma namjin kokarinsa ta fannin samar da hadin kai a tsakanin al'ummar musulmin duniya baki daya. Ayatullah Sayyed Fadlallah ya yi rubuce-rubuce da kuma fitar da fatawowi da dama cikinsu kuwa har da fatawar haramta kai hare-hare kunar bakin wake da wasu kungiyoyi ke yi da sunan musulunci.
An dai haifin marigayi Shehin Malamin ne a garin Najaf da ke kasar Iraki, kafin ya yi hijira zuwa kasar Labanan a cikin shekarar 1952.

609869
captcha