Wasikar da shugaban na Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ya aike ga shugaban kasar Lebanon Micheal Sulaiman ta kunshi cewa: " Abu ne da babu kokonto a ciki cewa rawar da wannan babban malamin ya taka a fagen hadin kan al'ummar kasa da kuma gwagwarmaya za ta shiga cikin shafukan tarihin kasar Lebanon."
A cikin sakon da ya aikewa iyalan mamacin, shugaba Mahmud Ahamdi Nejad ya ce: Rashin wannan babban marja'in asara ce mai girma na cibiyoyin ilimi na Hauza."
Shima shugaban Majalisar Fayyace maslahar musulunci ta Iran, Ayatullah Akbar Hashimi Rafsanjani ya bayyana Allamah Muhammad Hussaini Fadlallah a matsayin ma'abocin jihadi wanda ya kare rayuwarsa wajen kare musulunci da kuma kasarsa.
A jiya lahadi ne Allah ya yi wa Ayatullah Sayyid Muhammad Hussain Fadlallah rasuwa yana dan shekaru saba'in da biyar. A gobe talata ne za a yi jana'izarsa a babban birnin kasar Lebanon Beirut.
610025