Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muslim an bayyana cewa, kimanin dalibai maza da mata 117 ne suka hardace kur'ani baki dayansa a wani shirin bayar da horo da ake gudanarwa na hardar kur'ani mai tsarki a yankin zirin Gaza.
Ma'iakatar kula da harkokin addinin musulunci ta yankin zirin Gaza ita ce ta dauki nauyin gudanar da wannan shiri, inda yanzu haka akwai daruruwan daliban da suke cikin bayar da himma wajen hardar kur'ani mai tsarki.
Kakakin ma'ikatar kula da harkokin addini ta yankin Gaza ya fadi cewa, an yi amfani da hanyoyi na zamani wajen koyar da daliban, kuma a cikin ikon Allah an samu nasara.
610048