Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na tayyibun ya bayyana cewa za a gudanar da wani shiri na bayar da horo kan ilmin ka'idojin karatun kur'ani mai tsarki ko kuma tajwidi a birnin London na kasar Birtaniya a cikin wannan wata. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri zai mayar da hankali kan kaidojin karatun kur'ani ne da nufin samun makaranta gogaggu masu yawa a cikin kasar ta birtaniya, ta yadda musulmi za su alfahari da hakan.610017