Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran harkokin kur'ani na muzn an habarta cewa, an bude wani shiri na bayar da horo kan sahihan hukunce-hukuncen karatun kur'ani mai tsarki a wurare masu da ke cikin larduna da garuruwa daban-daban na kasar Iraki musamman ma a kudancin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa shirin yana da dangantaka kai tsaye da kokarin da cibiyoyin kur'ani na kasar ke yi wajen ganin an bunkasa harkokin kur'ani, kama daga bangaren tilawa har zuwa harda, wanda dukkaninsu suna bukatar lakantar ka'ida ta karatun kur'ani baki daya.
Ynzu ahka daia an fara gudanar da shirin tun kimanin kwanaki biyu da suka gabata, kuma za a kammala shirin baki daya a karshen bazarar wannan shekara. Babban daraktan cibiyar da ke jagorantar shirin ya sheda wa mane ma labarai cewa za a ci gaba da gudanar da shi a kowace shekara.
610443