Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar jamaran an bayyana cewa, Sayyid Hassan Khomeini ya aike da sakon ta'aziyar rasuwar babban malamin addinin Musulunci na kasar Labanan Ayatollah Sayyid Muhammad Hussein Fadlollah wanda Allah ya yi rasuwa tun ranar lahadi da ta gabata.
Bayanin ya ci gaba da cewa an aike da sakon ta'aziyar ne zuwa ga babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Labanan Sayyid Hassan Nasrallah tare da majalisar koli ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ke kasar.
610779