Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar kula da bunkasa harkokin ilmi da ala'dun Musulunci isesco.org, an bayyana cewa za a bude wata cibiyar gudanar da bincike kan harkokin tarihi da suka danganci Musulunci a jami'ar muuslunci da ke kasar Uganda da ke gabacin nahiyar Afirka wadda a kungiyar ta budea shekarun baya.
A wani bangaren labarin an bayyana cewa kungiyar ta isesco yana yin matukar koakrinta ne da nufin ganin an kiyaye dukkanin lamurra da suka danganci tari da ke da dangantaka da musulmin gabacin nahiyar Afirka, da suka hada da kasar ta Yganda da ma wasu daga cikin kasashen da ke da yawan musulmi.
610468