IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Kur'ani Mai Tsarki A Kasar Turkiya

20:19 - July 07, 2010
Lambar Labari: 1953230
Bangaren kasa da kasa; Ana shirin kammala kawo karshen taron kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Istanbul na kasar Turkiya kan alkur'ani mai tsarki da koyarwarsa ga bil adama.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labarai da ya samu daga bangaren da ke kula hulda da jama'a na ISESCO an bayayna cewa, ana shirin kammala kawo karshen taron kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Istanbul na kasar Turkiya kan alkur'ani mai tsarki da koyarwarsa ga bil adama a fadin duniya.

Bayanin ya ci gaba da cewa taron wanda ya samu halartar makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki gami dam asana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da ma wasu kasashen da ba na musulmi ba, mayar da hanakali ne kan irin yadda za a iya koyon dukkanin darussa na rayuwa daga koyarwar kur'ani mai tsarki a dukkanin sassa na rayuwar dan adam.

610468



captcha