IQNA

Ana Gudanar Da Makoki A Fadin Kasar Labanan

20:19 - July 07, 2010
Lambar Labari: 1953233
Bangaren siyasa da zamantakewa; Majalisar ministocin kasar Labanan ta bayyana ranar Talata a matsayin ranar makoki a fadin kasar, domin gudanar da janazar marigayi Allamah Sayyid Muhamamd Hussein Fadlollah da Allah ya yi wa rasuwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da bangaren hulda da jama'a na gwamnatin kasar Labanan ya bayar an bayyana cewa, majalisar ministocin kasar Labanan ta bayyana ranar Talata a matsayin ranar makoki a fadin kasar, domin gudanar da janazar marigayi Allamah Sayyid Muhamamd Hussein Fadlollah da Allah ya yi wa rasuwa tun ranar lahadi da ta gabata. Bayanin ya kara da cewa dubban daruruwan mutane na ciki da wajen kasar Labanan suka gudanar da janazar babban malamin a jiya.

610506




captcha