IQNA

An Rufe Marigayi Allamah Fadlollah A Masallacin Imamain Hasnain (AS)

20:15 - July 07, 2010
Lambar Labari: 1953234
Bangaren siyasa da zamantakewa; An bizne marigayi Allamah Sayid Muhammad Hussein Fadlollah a cikin masallacin Imamain Alhasnain (AS) da ke yankin kudancin birnin Beirut.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a rahoton da ya nakalto daga reshen yada labarai na ofishinsa da ke kasar Lababanan an bayyana cewa, an bizne marigayi Allamah Sayid Muhammad Hussein Fadlollah a cikin masallacin Imamain Alhasnain (AS) da ke yankin kudancin birnin Beirut fadar mulkin kasar ta labanan.

Rahoton ya kara da cewa tun bayan kammala janar Allamah Fadlollah a yammcin jiya, dubban mutane daga ciki da wajen kasar Labanan suna ci gaba da isa masallacinsa da ke yankin kudancin Beirut, domin yin ta'aziyya ga iyalansa. Allamah Sayyid Muhammad Hussein Fadlollah ya rasu ne a ranar Lahadi da ta gabata, bayan fama da rashin da rashin lafiya.

Dubban daruruwan mutane ne suka gudanar da janazar babban malamin a jiya Talata, tare da halartar manyan malamai da jami'ai daga sassa daban-daban na kasar da wajenta. Allamah Sayyid Fadlollah ya samu kyakkyawan yabo daga al'ummar kasar Labanan da malaman addinin Musulunci daga kasashen duniya, dangane da matsayinsa na neman hadin kan al'ummar musulmi, tare da fahimtar juna tsakanin musulmi da sauran mabiya addinai, da kuma yadda yake sukar siyasar zalunci da danniya ta gwamnatin yahudawan sahyuniya, kan al'ummar palastinu da sauran sauran musulmi.

610478



captcha