IQNA

An Bude Cibiyar Kur'ani Ta Hidaya A Kasar Jordan

20:19 - July 07, 2010
Lambar Labari: 1953235
Bangaren kur'ani; An bude wata babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani mai tsarki a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan, wadda wata cibiyar kula da ayyukan alhairi ta kasar ta dauki nauyin ginawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga banagaren yada labaransa na kasar Jordan an habarta cewa, an bude wata babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani mai tsarki a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan, wadda wata cibiyar kula da ayyukan alhairi ta kasar ta dauki nauyin ginawa tare da daukar nauyinta.

Bayanin ya kara da cewa cibiyar za ta mayar da hanakali ne wajen koyar da karatun kur'ani da harda, tare da koyar ilmomin kur'ani gami da ilmin ka'idojin karatun kur'ani mai tsarki wato tajwidi.

Cibiyar ta samu karbuwa daga musulmin kasar Jordan wadanda suka nuna a shirye suke su bayar da 'ya'yansu domin samun horon karatun kur'ani da harda, gami da sauran ilmomin da za a koyar a cibiyar.

610570


captcha