IQNA

Ya Kamata Al'ummar Musulmi Sun Nuna Ma'anar Ayar Hadin Kai A Aikace

11:16 - July 11, 2010
Lambar Labari: 1954031
Bangaren kasa da kasa; Wani makarancin kur'ani mai tsarki dan kasar Iraki ya kirayi al'ummar musulmi zuwa ga bayyana ma'anar ayar hadin kai tsakaninsu a aikace ba karantawa kawai ba aiki ba.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da Hashim Isma'il Salman, makarancin kur'ani mai tsarki dan kasar Iraki ya kirayi al'ummar musulmi zuwa ga bayyana ma'anar ayar hadin kai tsakaninsu a aikace ba karantawa kawai ba aiki ba kamar yadda ake gani a halin yanzu.

Makarancin ya ce al'ummar musulmi suna bukatar hadin kai a tsakaninsu a wannan zamani fiye da kowane lokaci, domin kuwa a yanzu ne ake yi wa musulmi barazana ta neman murkushe su ta kowace hanya, matukar dai ba su mika kai ga manufofin 'yan mulkin mallaka ba, wanda kuma yin hakan ne zai raba su da addininsu.


Daga karshe ya jinjina wa shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad kan namijin kokarin da yake yi wajen fadakar da al'ummar musulmi kan su farga da makircin 'yan mulkin mallaka.

612556


captcha