Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran haberfx an bayyana cewa, an gudanar da taron khatmar kur'ani mai tsarki a birnin Siirt na kasar Turkiya, wanda ya samu halartar makaranta daga sassan kasar a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da taron khatmar ne tare da halartar mahardata kur'ani fitattu, wanda cibiyar kula da harkokin matasa ta kasar ta shirya gudanarwa, da nufin kara fadakar da matasa kan muhimmancin karatu da hardar kur'ani mai tsarki, wanda hakan zai ba su damar komawa zuwa hakinin tarbiya ta Musulunci.
A lokacin da aka kammala taron khatmar an gudanar da addu'oi musamman ma ga al'ummar musulmi da suke fuskatar matsaloli a palastinu da sauran yankunan duniya kan Allah madaukakakin sarki ya ba su mafita.
612463