Bangaren kasa da kasa; Mutanen kasar Haddaiyar daular larabawa sun yi na'am da sabon tsarin nan hardar kur'ani mai tsarki na sarkin Al Zaid, wanda za a yi amfani da hanyoyi na zamani domin aiwatar da shi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar alittihad a shafinta na yanar gizo an habarta cewa, mutanen kasar Haddaiyar daular larabawa sun yi na'am da sabon tsarin nan hardar kur'ani mai tsarki na sarkin Al Zaid, wanda za a yi amfani da hanyoyi na zamani domin aiwatar da shi musamman ma a wannan lokaci.
Bayanin ya ci gaba da cewa yin amfani da wannan sabuwar hanya ta hardar kur'ani mai tsarki zai taimaka matuka wajen samar da mahardata cikin kankanin lokaci. Kuma wasu masu sha'awar yin amfani da shi a wajen kasar ma za su iya amfana.
612405