IQNA

An Fara Wani Shirin Horar Da Mahardata Kur'ani Saudiyya

11:17 - July 11, 2010
Lambar Labari: 1954043
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani shiri na horar da mahardata kur'ani mai tsarki a kasar Saudiyya a cikin shirin da ake gudanarwa a kowace a lokutan hutun bazara.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nasij an bayyana cewa, an fara gudanar da wani shiri na horar da mahardata kur'ani mai tsarki a kasar Saudiyya a cikin shirin da ake gudanarwa a kowace a lokutan hutun bazara da ake bayarwa a kasar.

Shugaban hukumar kula da hrkokin kur'ani na kasar Saudiyya Abdullah bin Ali Algamidi ya bayyana cewa, wannan shiri yana da matukar muhimmanci, duk da cewa za a gudanar da shi ne acikin kankanin lokaci amma zai bayar da dama ga masu sha'awa su koyi abubuwa da dama.

612389



captcha