Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yanar gizo na zenebiye ya habarta cewa, mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah na kasar turkiya sun gudanar da tarukan ranar idin mab'a na tunawa da ranar aiko manzon Allah (SAW) a birnin Istanbul fadar mulkin kasar ta Turkiya.
Byanain ya ci gaba da cewa mabiya tafarkin iyalan gidan manzon suna gudanar da irin wadannan taruka a kowace shekara, wanda cibiyar kula da harkokin al'adu take daukar nauyin gudanarwa a babban masallacin zenebiye da ke birnin Istanbul.
A lokacin gudanar da tarukan an gabatar da jawabai kan matsayin wannan rana a addinin Musulunci da ma tarihin dan adam, wanda ke tabbatar da cewa addinin Musulunci addini ne daga cikin fitattun addinai da aka safkar daga sama.
612332