Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren hulda da jama'a na kungiyar ISESCO ya habarta shafin sadarwarsa na yanar gizo cewa, kwamitin zartarwa na kungiyar bunkasa harkokin ilmi da ala'du na kasashen musulmi ya gudanar da zamansa karo talatin da daya a birnin Ribat na kasar Morocco fadar mulkin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa mambobin kwamitin da suka hada da kasashe da dama daga cikin kasashen larabawa da na musulmi sun mayar da hanakali kan muhimman batutuwa na habbaka ilmi a kasashen musulmi, tare da hada karfi da karfe wajen taimaka ma masu rauni daga cikinsu.
612333