IQNA

An fara Taron Kungiyoyin Musulmin Kasar Spain

19:42 - July 11, 2010
Lambar Labari: 1954236
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da taron kungiyoyin musulmin kasar Spain a birnin Madrid fadar mulkin kasar, wanda shi ne irinsa na ashirin da takwas da ake gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ucide an bayyana cewa, an fara gudanar da taron kungiyoyin musulmin kasar Spain a birnin Madrid fadar mulkin kasar, wanda shi ne irinsa na ashirin da takwas da ake gudanarwa a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa musulmin kasar Spain suna gudanar da irin wadannan tarukan ne duk shekara, domin tattauna muhimman batutuwa suka shafi harkokinsu a kasar, da suka hada da yanayin rayuwarsu, 'yancinsu na gudanar da harkokin addini da dai sauransu.

Har ila yau a irin wadannan tarukan ne suke duba irin nasarorin da suka samu wajen gudanar da ayyukansu na addini da kuma matsalolin da suka samu, tare da tattauna hanyoyinsu warware su a gaba.

612350


captcha