IQNA

Gasar Isra'i Da Mi'iraji Ta Yanar Gizo A Kasar Kuwait

19:41 - July 11, 2010
Lambar Labari: 1954238
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da gasar isra'i da mi'iraji ta hanyar yanar gizo a kasar Kuwait, wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar ta shirya domin tunawa da zagayowar ranar aiko ma'aiki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait Kuna cewa, An fara gudanar da gasar isra'i da mi'iraji ta hanyar yanar gizo a kasar Kuwait, wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar ta shirya domin tunawa da zagayowar ranar aiko ma'aiki (SAW)

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan matsayi da al'ummar musulmi suka kai na gudanar da gasa domin kara fitar da ilmomi da ke tattare da sirrin aiko ma'aiki (SAW) zuwa ga bil adama, na da babban tasirin a makomar al'ummar musulmi ta fuskacin ilmi da yawaita kara bunkasa hanyoyin bincike.

612367




captcha