IQNA

Turkiya Za Ta Dauki Nauyin Bakuncin Baje Kolin Kayan Halal

20:27 - July 13, 2010
Lambar Labari: 1955263
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani taron baje kolin kayyakin halal a Musulunci nan da watanni biyu masu zuwa a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, wanda za a gudanar a matsayi kasa da kasa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran gidaraporu ya habarta a shafinsa na yanar gizo cewa, za a gudanar da wani taron baje kolin kayyakin halal a Musulunci nan da watanni biyu masu zuwa a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, wanda za a gudanar a matsayi kasa da kasa a birnin.

Yanzu haka dai kimanin kasashe arba'in daga cikin kasashen musulmi ne suka bayyana aniyarsu ta halartar wannan babban baje koli na kayyakin halal, gami da wasu kasashe dab a na musulmi amma suna da kyakkyawar danganta ta harkokin kasasunci da kasashen musulmi da suka hada da China da kuma Holand gami da kasar Birtaniya.

Daga cikin kasashen musulmi da za su halarci taron baje kolin akwai jamhuriyar Musulunci ta Iran, hadaddiyar daular larabawam Syria, Indonesia, Iraki da kuma Saudiyya.

612615


captcha