IQNA

Gasar Harda Da Karatun Kur'ani Ta Mata A Karon Farko A Kutaif

20:27 - July 13, 2010
Lambar Labari: 1955265
Bangaren kasa da kasa; Babbar cibiyar nan ta darul kur'an ta yankin Kutaif a gabacin kasar saudiyya ta shirya gudanar da wata gasar harda da kuma karatun kur'ani a karon farko da ta kebanci mata a yankin.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga kamfanin dillancin labaran kur'ani na muzn cewa, babbar cibiyar nan ta darul kur'an ta yankin Kutaif a gabacin kasar saudiyya ta shirya gudanar da wata gasar harda da kuma karatun kur'ani a karon farko da ta kebanci mata a yankin, wadda za a gudanar a cikin watan ramadana mai zuwa.

Bayanin ya ce za a gudanar da gasar ne bisa matakai, inda daga karshe za a sanar da sunayen wadanda za su kai mataki na kusa da karshe, daga nan kuma za a fitar da wadanda za su je ga matakin karshe.

An kasa masu shiga gasar daidai shekarunsu, inda kanan yara daga cikinsu za su fara daga izihi na daya, masu biye musu kuma daga juzu'I na biyu zuwa sama, kuma za a fitar na daya da na biyu da uku daga kowane bangare bisa la'akari da shekaru.

612861



captcha