Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa; a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na tayyibun na yanar gizo an habarta cewa, ana shirye-shiryen gudanar da wani shirin koyar da ilmomin addinin Musulunci a birnin London na kasar Birtaniya a cikin watan Ramadana mai zuwa na wannan shekara da muke ciki.
Rahoton ya ci gaba da cewa cibiyar kula da harkokin Musulunci ta birnin London ita ce ta dauki nauyin gudanar da wannan shiri, wanda zai samu halartar musulmi da dama. Yanzu haka dai an fara gudanar da rijistar wadanda za su halarci wannan shiri, wadanda dukkaninsu musulmi na kasar Birtaniya da suka fito daga sassa daban-daban na kasar.
Daga cikin muhimman abubuwan da za a koyar a shirin akwai kyatata karatun kur'ani mai tsarki, tare da sani ma'anonin wasu daga cikin ayoyin kur'ani da kuma hadisan ma'aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare da iyalna gidansa.
612666