IQNA

An Raba Kwafin Kur'anai Sama Da 3000 A Kasar Turkiya

20:26 - July 13, 2010
Lambar Labari: 1955267
Bangaren kasa da kasa; An raba kwafin kur'ani mai tsarki sama da dubu uku a sassa daban-daban na birnin Istanbul na kasar Turkiya , wanda kwamitin kula da harkokin matasa na kasar ya dauki nauyi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na Yeni Asya ya habarta cewa, an raba kwafin kur'ani mai tsarki sama da dubu uku a sassa daban-daban na birnin Istanbul na kasar Turkiya , wanda kwamitin kula da harkokin matasa na kasar ya dauki nauyin aiwatarwa.

Bayanin ya kara da cewa an rarraba kwafi-kwafin na kur'anan ne ga matasa masu halartar azuzuwan koyon karatun kur'ani mai tsarki a makarantun addini da ke cikin birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya.

Wannan yana daya daga cikin muhimman ayyukan da kwamitin kula da harkokin matasa na kasar ke gudanarwa da nufin kara jawo hankulan matasa zuwa ga harkokin addini, da kuma koyon karatun kur'ani mai tsarki.

612645



captcha