IQNA

Za A Gina Wani Masalalci A Birnin Cambridge Na Birtaniya

23:52 - July 14, 2010
Lambar Labari: 1956046
Bangaren kasa da kasa; Za a gina wani babban masallci a birnin Cambridge na kasar Birtaniya bisa koyarwar kur'ani mai tsarki dangane da kare mahalli a matsaki na rayuwar zamantakewar al'umma.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na treehugger an bayyana cewa, za a gina wani babban masallci a birnin Cambridge na kasar Birtaniya bisa koyarwar kur'ani mai tsarki dangane da kare mahalli a matsaki na rayuwar zamantakewar al'umma daidai da mahangar addinin musulunci.

Bayanin ya kara da cewa babbar cibiyar kula da harkokin kula da kare mahalli ta kasar Birtaniya wadda take da manyan ofisoshi a fadin kasar, ita ce ta dauki nauyin gina wannan masallaci, wanda zai lashe kudade har pound miliyan uku.

Yanzu haka cibiyar kula da harkokin musulunci ta kasar Birtaniya ta yi na'am da wannan mataki, inda ta bayyana cewa koyarwar kur'ani mai tsarki a koda yaushe daidai take da maslahar dan adam a cikin dukkanin lamurran rayuwarsa.

613815







captcha