IQNA

Taron Kasashen Musulmi Da Na Wadanda Ba Na Musulmi Ba A Singapour

23:52 - July 14, 2010
Lambar Labari: 1956048
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zama na kasashen musulmi da na wadanda ba na musulmi a kasar Singapour, wanda za a gudanar a matsayi na kasa da kasa tare da halartar wakilai daga kasashe da dama.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar straits news cewa cewa, za a gudanar da wani zama na kasashen musulmi da na wadanda ba na musulmi a kasar Singapour, wanda za a gudanar a matsayi na kasa da kasa tare da halartar wakilai daga kasashe da dama na mabiya addinin musulunci da kuma wasu na gabacin nahiyar Asia.

Bayanin ya kara da cewa kimanin masana 250 ne daga kasashen duniya za su halarci wannan zaman taro,inda za su gabatar da bayani dangane da muhimmancin da ke tattare da hada karfi da karfe wajen bunkasa huldodi tsakanin kasashen musulmi da sauran kasashe.

613624










captcha